Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta gargaɗi ƴan Najeriya da su kiyaye wajen mu’amala da katin ATM domin guje wa faɗawa tarkon masu zamba ta yanar gizo da ke amfani da bayanan katin domin kwashe kuɗi daga asusun mutane.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Bright Edafe, ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Da fatan za ku kula da katin ATM ɗinku. Hoton bayanan katin kaɗai na iya sa su sace maka kuɗi. Ba sai sun mallaki pin ko wayarka ba. Ba lallai ne su samu OTP ba. Abin da za ka gani kawai shine cira bayan cira har sai an gama da duk kuɗinka. Ka kiyaye katinka, kada ka ba wani domin yai maka sayayya. Kada ka ce ƴansanda ba su sanar da kai ba.”
KARANTA WANNAN: YANZU-YANZU: Sojoji Na Artabu Da Ƴan ISWAP A Yobe
Wannan gargaɗi na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake samun ƙaruwar damfarar yanar gizo da ake amfani da fasahar zamani wajen tsallake na’urar tsaro na bankuna.