Najeriya na ƙara ƙaimi wajen karkata ga amfani da makamashi mai tsabta tare da kare matakin ta na tura wutar lantarki zuwa ƙasashe makwabta duk da cewa miliyoyin ƴan ƙasa ba su da isasshiyar wutar.
Daraktan Hukumar Makamashi ta Ƙasa (ECN), Mustafa Abdullahi, ya shaida wa Channels Television cewa, kashi shida cikin ɗari ne kacal na wutar da ake samarwa ake bai wa ƙasashe irin su Benin, yana mai bayyana hakan a matsayin “manufa ta dabaru” don guje wa rikici kan madatsun ruwa da ake amfani da su tare.
Ya ce: “Ba za mu iya raba koguna da madatsun ruwa da wata ƙasa ba mu ba su wuta a matsayin kyautatawa ba,” yana mai gargaɗin cewa ƙin yin hakan na iya jawo matsalar ababen more rayuwa mai tsanani.
Abdullahi ya bayyana cewa yanzu kashi 60 cikin 100 na ƴan Najeriya na samun wuta, daga sama da megawatt 4,000 a 2023 zuwa megawatt 6,000 a yanzu, sai dai ya amince da cewa: “Ba mu kai inda ya kamata ba tukuna, amma manufofinmu da hangen nesanmu za su kai mu wajen.”
Ya danganta matsalar yawan katsewar wuta ga tsofaffin layukan rarraba wutar da dogaro sosai kan iskar gas da ruwa, tare da alƙawarin “samar da tsarin solar kusan a duk fadin ƙasar” da kuma faɗaɗa sauran hanyoyin samar da wutar.
Sabuwar Dokar Wuta ta bai wa jihohi damar samarwa, rarrabawa da kuma tsara wutar lantarki, amma mafi yawansu na farawa da aikin gwaji na megawatt biyar kacal saboda ƙarancin ƙwarewa.
Binciken makamashi ya nuna cewa kashi 86 cikin 100 na wutar na fitowa ne daga iskar gas, kashi 12 daga ruwa, sannan “ƴar kaɗan” daga makamashi mai tsafta, lamarin da ya sa aka buƙaci a canza kayan amfani da wutar zuwa masu ƙarancin shan makamashi.
Abdullahi ya kare tsarin Band A/B da ake kokawa a kai, yana mai cewa na wucin gadi ne kuma za a kawar da shi idan an ƙara ƙarfin wutar daga tsarin makamashin mai tsafta: “Wutar lantarki ba ta da arha ko’ina a duniya – lokacin samun rangwame ya ƙare ga ƴan Najeriya.”
Ya kuma yi alfahari da shirin samar da motocin lantarki, yana mai cewa hukumar ta daina sayen motar fetur kuma tana bayar da caji kyauta ga jama’a domin nuna cewa “abu mai yiwuwa ne” a daina dogaro a kan mai.