Shugaban Ƴan Wasan Najeriya, Ahmed Musa ya bayyana cewa, ya rage farashin fetur ne a gidan mansa MYCA-7 da ke Kano domin ya temaka wajen rage raɗaɗin da ƴan Najeriya ke sha saboda janye tallafin man fetur.
Ahmed Musa dai ya sanar da rage farashin man daga naira 620 zuwa 580 a kowacce lita ne ranar Litinin da ta gabata a shafinsa na Twitter.
Da yake magana da wakilin PUNCH a jiya Laraba, ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sivasspor ta Turkiya ya ce, ya yi hakan ne domin ya bayar da gudunmawa wajen rage raɗaɗin da talakawa suke sha.
“Shine abu mafi dacewa da zan iya yiwa mutane na a nan,” in ji Ahmed Musa.
“Komai ƙanƙantar ragi, zamu more shi. Abubuwa sun yi ƙamari yanzu kuma na san mutane suna fama a kullum wajen ganin sun rayu.”
Labari Mai Alaƙa: CIRE TALLAFI: Gidajen Mai Sun Fara Shirin Korar Ma’aikata
Ahmed Musa ya kuma bayyana fatansa na buɗe ƙarin gidajen mai a faɗin Najeriya kafin ya yi ritaya daga buga ƙwallon ƙafa.
“Ina sa ran, MYCA-7 zai kasance a sauran sassan Najeriya nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Ɗan wasan mai shekaru 30 a duniya, shine ɗan wasan Najeriya mafi samun yabo, kasancewar ya buga wasanni 108 tun lokacin da ya bayyana a shekarar 2010, lokacin yana ɗan shekaru 17 kacal.
Ya ji ƙwallo 16 a kulof ɗinsa na ƙasa, abin da ya sa kulof ɗin lashe Gasar Cin Kofin Afirka ta shekarar 2013, sannan kuma ya buga Gasar Duniya har sau biyu.
Ahmed Musa ya ci wa Najeriya wasa sau biyu a Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 2014 da Gasar Cin Kofin Duniya ta 2018, abin da ya sa ya zama ɗan Najeriya mafi cin ƙwallo a Gasar Cin Kofin Duniya, inda yake da ƙwallo huɗu.