Damagun Na Fuskantar Matuƙar Matsi Kan Ya Kira Taron Shugabannin PDP Na Ƙasa

Mai Riƙon Muƙamin Shugabancin Jam’iyyar PDP, Umar Damagun, na fuskantar matsi kan ya kira taron Shugabannin Jam’iyyar na Ƙasa.

Tun bayan naɗinsa a matsayin mai riƙon shugabancin jam’iyyar a watan Maris na wannan shekarar, Damagun bai samu damar kiran taron shugabannin jam’iyyar ba, abun da ake alaƙantawa da dalilai da dama, waɗanda a wani lokacin ake ganin sun fi ƙarfin shi Damagun ɗin.

Da yake nuna rashin gamsuwarsa da yanayin da ake ciki, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023 da ya gabata, Atiku Abubakar, ya kira taron tattaunawa na wasu manyan jam’iyyar domin fitar da hanyar da za a bi wajen farfaɗo da jam’iyyar.

KARANTA WANNAN: PDP Ta Ƙirƙiri Kwamiti Na Musamman Kan Zaɓen Jihohin Bayelsa, Imo Da Kogi

Sati guda bayan wannan ne kuma, Atiku da wanda yai masa takarar mataimaki, Ifeanyi Okowa suka gana da gwamnonin PDP, wakilan ƴan kwamitin amintattu da kuma ƴan kwamitin gudanarwa na ƙasa a Abuja, inda duk shugabannin suka nuna cewar ba zasu lamunci duk wani yunƙuri na yi wa PDP zagon ƙasa ba.

Da yake magana kan lamarin a Abuja, Mataimakin Shugaban Matasa na Ƙasa na PDP, Timothy Osadolor ya ce, waɗanda ke son a kira zaman shugabannin jam’iyyar zasu iya samun biyan buƙatarsu kwanannan.

Ya ce, manyan jam’iyyar da dama na son a kira zaman da gaggawa, inda ya bayyana hakan a matsayin abu mai muhimmanci saboda a duba abubuwan da suka faru a jam’iyyar.

Ya kuma ce, taron shugabannin jam’iyya abu ne da yake buƙatar shiri da tsari na musamman, inda ya ce, ba abu ne da kawai za a kira saboda wasu sun ce kawai a kira ba.

Wani babban ɗan jam’iyyar PDP daga yankin Kudu Maso Yamma, ya ce, matuƙar Damagun bai kira taron shugabannin jam’iyyar ba, to akwai alamun tambaya a kan shugabancinsa.

PDPUmar Damagun
Comments (0)
Add Comment