Darajar Naira Ta Ƙara Rugujewa Inda Ake Canja Dala 1 Kan Naira 1,660

Jiya, darajar Naira ta ƙara faɗuwa zuwa N1,660 kan dalar Amurka a kasuwar bayan-fage daga N1,645 da aka samu ranar Juma’ar da ta gabata.

Sai dai kuma, darajar Nairar ta ƙaru zuwa N1,580.46 kan dalar Amurka a kasuwar musayar kudade ta ƴan kasuwa ta Najeriya (NAFEM).

Bayanan da aka samu daga FMDQ sun nuna cewa farashin musayar kuɗi a NAFEM ya faɗi zuwa N1,580.46 kan dalar Amurka daga N1,593.32 da aka samu karshen makon da ya gabata, wanda ya nuna ƙaruwar darajar Naira da N12.86, duk da raguwar cinikin daloli da kashi 22 cikin 100 zuwa dala miliyan 197.37 daga dala miliyan 254.17 da aka yi ciniki a karshen makon da ya gabata.

A sakamakon haka, giɓin tsakanin farashin kasuwar bayan-fage da na NAFEM ya ƙara faɗaɗa zuwa N79.54 kan dalar Amurka daga N51.68 kan dalar Amurka a Juma’ar da ta gabata.

Darajar Naira
Comments (0)
Add Comment