Dole PDP Ta Yunƙura Yanzu, Ta Jurewa Wike Tsawon Lokaci, Inji Tsohon Shugaba A Jam’iyyar

Tsohon Mai Binciken Kudi na Ƙasa a jam’iyyar PDP, Barista Ray Nnaji, ya ce jam’iyyar ta daɗe tana haƙuri da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.

Nnaji ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi, inda ya yi tsokaci kan rikicin da ke addabar jam’iyyar ta PDP.

Wannan na faruwa ne a lokacin da Wike ya soki shugabannin PDP, yana ƙalubalantar su kan kiransa karen farautar wata jam’iyyar.

Minista Wike ya bayyana hakan ne a wani shirin talabijin, yana mai cewa ba ya jin tsoron duk wanda zai zarge shi.

Duk da haka, Nnaji ya koka da halin da jam’iyyar ke ciki, yana cewa babu wani mamba na PDP da zai yaba da abin da ke faruwa a jam’iyyar.

Ya kuma ƙara da cewa, jinkirin sauƙe tsohon Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Iyorchia Ayu ne ya haifar da wannan rikici.

Nnaji ya yi kira ga jam’iyyar ta gaggauta gyara gida, idan har tana so ta sake dawowa kan hanya.

Ya kuma bayyana cewa, Wike yana son amfani da ƙarfinsa a jihar Ribas don cimma burinsa a 2027.

A ƙarshe, ya ce jinkirin da jam’iyyar tayi wajen daukar mataki ya ba Wike dama ya yi tasiri sosai cikin jam’iyyar.

Nyesom WikePDP
Comments (0)
Add Comment