Daily Trust ta tabbatar da cewa Abubakar Abba, jagoran sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna Mahmuda, yana hannun Hukumar Tsaro ta DSS bayan an cafke shi a Jihar Neja.
An gano cewa wannan shugaban ta’addanci, wanda jami’an sirri suka kama a Wawa, ƙaramar hukumar Borgu, ya jagoranci hare-hare daban-daban a sassan Arewa ta Tsakiya, ya kuma shimfiɗa ta’addancinsa zuwa Kwara, Kogi da Nasarawa.
Mai magana da yawun Gwamnan Neja, Bologi Ibrahim, ya bayyana kama mutumin a matsayin babbar nasara a yaƙi da ta’addanci, kamar yanda rahoton Daily Trust ya nuna.
Rahoton ya ce wasu yankuna, musamman Shiroro, sun sha hare-hare tare da faɗawa tarkon da aka yi wa jami’an tsaro, abin da ya haifar da asarar rayuka da samun jikkata.
A ranar 3 ga Yuni, aƙalla ƴan sa-kai 15 aka kashe a Kemanji, lamarin da ya ƙara nuna tsananin barazanar ƙungiyar ga al’umma.
Shaidu sun ce mayaƙan su kan bayyana cikin kayan soji suna hawa babura yayin kai farmaki, inda suke aikata kisan gilla, sace-sace, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ƙaƙaba haraji na tilas.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa Daily Trust cewa “an riga an fara abin da ya kamta bayan kamun; irin bayanan sirrin da suka kai ga kama shi za su taimaka wajen kawo ƙarshen mulkin wannan sabuwar ƙungiya.”
Duk da binciken da ke gudana, ba a iya samun Ma’aikatar Tsaro ta cikin gida don karin bayani ba, kuma saƙon imel da aka aike da shi bai sami amsa ba zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoton.
Al’umma a yankunan da abin ya shafa na sa ran DSS ta gaggauta bankaɗo sauran mambobi da hanyoyin samun kuɗaɗensu, tare da tabbatar da tsaro ga manoma da mazauna karkara.