DSS Ta Kama Jami’in Gwamnati Da Karkatar Da Kayan Tallafin Rage Raɗaɗi

Rundunar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, ta kama wani ma’aikacin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Nasarawa da wasu mutane da yake aiki da su, bisa zargin karkatar da kayan tallafin da aka tanadarwa talakawan da ke cikin matsatsi.

Ana zargin mutanen ne da sayar da kayan tallafin a kasuwar zamani da ke Lafia da kuma sauran kasuwanni.

KARANTA WANNAN: Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Gidajen El-Rufai A Abuja, Sun Tafi Da Wani Magidanci

A wata sanarwa da ta fita a jiya Talata, Mai Magana da Yawun DSS, Peter Afunanya ya bayyana cewar, rundunar ta ƙwato wasu kayayyakin bayan ta yi bincike a kan lamarin.

Afunanya ya bayyana cewar, ana gudanar da irin wannan bincike a sauran jihohin da ke faɗin ƙasar nan.

Ya ƙara da cewar, DSS ta miƙa waɗanda ake zargin ga inda ya kamata su fuskanci hukuncin laifuffukan da su ka aikata.

DSSTallafi
Comments (0)
Add Comment