Dukkan PDP A Delta Ta Koma APC A Wani Babban Taron Siyasa Tare Da Kashim Shettima Da Ganduje

Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC tare da manyan magoya bayansu a wani babban taro da aka gudanar a filin Cenotaph, Asaba, babban birnin jihar.

A wurin taron, da aka samu halartar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, shugaban APC Abdullahi Ganduje, da sauran manyan ‘yan siyasa, an karɓi mutanen cikin girmamawa da farin ciki.

Oborevwori ya bayyana sauya shekar a matsayin “motsi” maimakon ficewa kawai, inda ya ce sun yanke shawarar ne bayan tuntubar masu ruwa da tsaki domin jin daɗin jihar Delta.

Gwamnan ya ce soyayya da shugaba Bola Tinubu ke nunawa jihar ta sa suka ga dole ne su haɗa kai da gwamnatin tarayya maimakon su ci gaba da zama ƴan adawa.

Okowa ma ya ƙarfafa wannan matsayi, inda ya ce matakin da suka ɗauka shi ne mafi alheri ga jama’ar jihar Delta, ba don kansu ba.

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa sun sauya sheƙa ne domin tabbatar da haɗin kai da ci gaban jihar Delta ta hanyar haɗa guiwa da gwamnati mai ci.

Mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya bayyana sauya sheƙar a matsayin wata babbar girgiza a tarihin siyasar yankin Kudu-Maso-Kudu da ma Najeriya baki ɗaya.

Comments (0)
Add Comment