EFCC Na Buƙatar Kotun Ƙoli Ta Janye Wankewar Da Aka Yi Wa Sule Lamido

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, EFCC, ta je Kutun Ƙoli tana buƙatar kotun da ta janye hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja ta yi ranar 25 ga watan Yuli a kan Sule Lamido, ƴanƴansa biyu da sauransu.

EFCC dai na zargin Sule Lamido ne da wasa da ofis a lokacin da yake gwamnan Jihar Jigawa a tsakanin shekarar 2007 da 2015, inda ya karkatar da kuɗaɗen tukuicin da yake samu daga kamfanonin da gwamnatin jihar ta ba su kwangila lokacin yana gwamna.

EFFC na kuma zargin Sule Lamido da haɗa kai da ƴanƴansa, Aminu da Mustapha da wani hadiminsa Aminu Abubakar da kuma kamfanonin Bamaina Holdings Ltd da Speeds International Ltd kan zarge-zarge 37 da ke da alaƙa da karkatar da kuɗin da yawansa ya kai naira biliyan 1.35.

To sai dai kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta wanke Sule Lamido da sauran waɗanda ake zargi a ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata bisa rashin samun cikakkiyar hujja daga ɓangaren EFFC kan zarge-zargen.

Bayanan ɗaukaka ƙarar da EFCC tai a ranar 31 ga watan Yuli, zuwa Kotun Ƙoli bisa rashin gamsuwa da hukuncin ranar 25 ga watan Yulin sun nuna cewa, EFCCn na buƙatar kotun da ta yi watsi da hukuncin tare da umartar ci gaba da yin shari’a kan zarge-zargen.

EFCCn ta ce hukuncin ta Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja ta yi, ta yi shi a kan kuskure lokacin da ta nuna cewa an fara shari’ar ne a Babbar Kotun Tarayya ta Abuja maimakon Babbar Kotun Tarayya ta Kano.

EFCCKotun KoliSule Lamido
Comments (0)
Add Comment