EFCC Ta Fara Bincike Kan Tsoffin Shugabannin NNPC Kan Badaƙalar Dubunnan Biliyoyi

Hukumar EFCC ta fara bincike mai zurfi kan zargin almundahana da amfani da ofis ba bisa ƙa’ida ba da ake yi wa wasu tsoffin manyan jami’an Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPC), ciki har da tsohon GMD, Mele Kyari, da Abubakar Yar’Adua.

A wata takarda da PREMIUM TIMES ta gani mai lamba CR:3000/EFCC/ABJ/HQ/SDC.2/NNPC/VOL.1/698, wanda aka aika wa shugabancin NNPC ranar 28 ga Afrilu, EFCC ta buƙaci a miƙa mata takardun albashi da alawus na jami’ai 14 ciki har da waɗanda suka riga suka yi ritaya.

A cewar takardar, “Duba da wanna takarda, ana buƙatarka da ka bayar da sahihan takardun bayanan albashi da alawuns, ciki har da waɗanda suka yi ritaya ba sa aiki da kamfaninka a yanzu.”

KARANTA WANNAN: Darajar Naira Ta Ƙara Faɗuwa A Kasuwar Gwamnati

Sunayen da ke cikin jerin sun haɗa da Mele Kyari; Ibrahim Onoja na PHRC; Mustafa Sugungun na KRPC; da wasu jami’ai 11 da suka haɗa da Umar Ajiya da Isiaka Abdulrazak.

Binciken yana da nasaba da kashe dala biliyan $2.896 da aka yi don gyaran matatun mai, ciki har da $1.56bn ga PHRC, $740.6m ga KRPC, da $656.9m ga matatar Warri.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da binciken, amma ya ce ba shi da cikakken bayani a halin yanzu.

A lokaci guda, ministan kuɗi Wale Edun ya bayyana cewa ana gudanar da binciken lissafin kuɗi na cikin gida (forensic audit) a NNPC, yana mai cewa “NNPC tana buƙatar samun ƙarin kuɗin shiga na daloli,” domin farfaɗo da tattalin arziƙin man fetur.

Comments (0)
Add Comment