Babban ɗan jam’iyyar PDP, Sanata Shehu Sani ya yi hasashen cewa, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i zai iya jawo rigima tsakanin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima
Da yake magana a gidan talabijin na Arise, tsohon ɗan Majalissar Dattawan ya bayyana rigimar da ta faru tsakanin tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo da mataimakinsa a matsayin wadda El-Rufa’i ya kitsa a matsayinsa na minista a lokacin.
Labari Mai Alaƙa: Akwai Wike, El-Rufai, Edun, Oyetola, Adelabu Da Sauransu A Sunayen Ministocin Tinubu
Shehu Sani yana da ra’ayin cewa, El-Rufa’i macijin ƙaiƙayi ne da aka shigo da shi cikin gwamnati mai ci, inda ya jaddada cewa, tsohon gwamnan zai haifar da rigima tsakanin shugaban ƙasa, ƴan majalissar zartarwa da kuma gwamnonin jihohi.
Sanata Shehu Sani ya kuma shawarci shugaban ƙasa da yai matuƙar kulawa, inda ya ce, duk wani daga ƴan majalissarsa da ya gagara taɓuka komai a cire shi a canza shi.