Ƙungiyar Tarayyar Turai, EU, ta ce ta dakatar da duk wani tallafi na kuɗi da take bai wa Nijar tare da yanke duk wata hulɗa a kan abin da ya shafi tsaro a tsakaninta da ita, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.
Jagoran manunfofin hulɗa da ƙasashe na EU, Josep Borrell ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
RFI Hausa ta rawaito cewa, waɗanda suka yi juyin Mulki a Nijar sun ayyana Janar Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaban ƙasa a ranar Juma’a, bayan da suka wancakalar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Mohammed Bazoum.
Tarayyar Turai, Amurka, ECOWAS, AU da sauran ƙasashen duniya sun yi kira da a saki shugaba Bazoum ba tare da gindaya wasu sharuɗa ba, sannan a maido da mulkin demokaraɗiyya a ƙasar.
RFI Hausa ta ce, Nijar ce kasar da ta fi samun tallafi daga ƙasashen Turai, kuma babbar abokiyar aikin EU a wajen yaƙi da bakin haure da ke bi ta sahara zuwa nahiyar Turai.
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta wallaafa a shafinta na intanet cewa, ta kasafta kuɗin da ya kai Yuro miliyan 503 tun daga shekarar 2021 don bunƙasa sha’anin mulki da ilimi a Jamhuriyar Nijar.