FIRS, Customs, NUPRC, NIMASA, da NNPC Zasu Fuskanci Cikakken Bincike Kan Hada-Hadar Kuɗaɗensu

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan dukkan cire kuɗaɗe da tsarin riƙe kudade da hukumomin tara kuɗaɗe ke yi, ciki har da FIRS, Customs, NUPRC, NIMASA, da NNPC.

Wannan mataki na nufin ƙara adana kuɗaɗe, inganta amfani da su, da samar da ƙarin kuɗaɗe domin bunƙasa tattalin arziƙi.

Tinubu ya ce a sake duba kaso 30% na kuɗin gudanarwa da kaso 30% na kuɗin fito NNPC ke karɓa ƙarƙashin Petroleum Industry Act.

Ya yaba wa kwamitin Zartarwa kan sauye-sauyen da suka kawo tsari na gaskiya da inganta zuba jari a ƙasar.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa ana kan hanyar gina tattalin arziƙin dala tiriliyan 1 zuwa 2030, inda ya jaddada cewa dole ne a samu ƙaruwar tattalin arziƙi aƙalla kaso 7% kowace shekara daga 2027.

Ya ce wannan ba kawai burin tattalin arziƙi ba ne, sai dai wani wajibi, domin ita ce hanya mafi ɗorewa wajen magance talauci.

Tinubu ya kuma bayyana shirin Renewed Hope Ward Development Programme domin tallafa wa mutane a matakin karkara.

Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya ce alamu na bunƙasar tattalin arziƙi suna inganta, haɗa da sauƙar hauhawar farashin kayayyaki da ƙaruwar kuɗaɗen shiga.

Edun ya ƙara da cewa binciken zai tabbatar da cewa kuɗaɗen da ake tarawa suna amfani wajen zuba jari cikin ƙasa da waje, musamman a fannin tituna da wutar lantarki.

Comments (0)
Add Comment