Fiye Da Mata 2,000 Sun Amfana da Tallafin Naira Miliyan 135 Daga Uwargidan Gwamnan Jigawa

Daga Mika’il Tsoho, Dutse

Fiye da mata 2,000 da marasa galihu a Jihar Jigawa sun amfana da tallafin Naira miliyan 135 daga uwargidan gwamnan jihar, Hajiya Hadiza Umar Namadi.

Shirin na nufin rage raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya haifar wa mazauna jihar.

Hajiya Hadiza Umar Namadi ta bayyana cewa an raba tallafin ga mata daga sassa daban-daban na jihar, tana mai gode musu bisa rawar da suka taka wajen nasarar jam’iyyar APC a zaɓen 2023 na ƙasa da na jiha.

“Mata sun taka muhimmiyar rawa, domin sun fito kwansu da kwarkwatarsu suka jefa kuri’unsu ga APC, suka jawo jam’iyyar ta yi nasara. Saboda haka, duk wani abu da aka yi musu ba kyauta ba ce, hakkinsu ne,” in ji ta.

Bugu da kari, sama da manyan mata 250 sun amfana da Naira 100,000 kowannensu karkashin shirin New Hope Initiative wanda uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Remi Bola Tinubu, ke jagoranta.

Wannan shiri yana daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na nuna godiya ga mata bisa goyon bayan da suke ba wa gwamnatin APC a matakin tarayya da jihohi.

Hajiya Hadiza ta kuma bayyana cewa an ware Naira miliyan 50 domin tallafa wa mata a jihar Jigawa daga Sanata Remi Bola Tinubu, tare da tallafi ga mata da ke aikin gona ta hanyar samar da kayan aiki kamar na’urar ban ruwa.

Gwamnatin Jihar Jigawa, ƙarƙashin Gwamna Umar Namadi, ta fifita inganta rayuwar mata.

A matsayin wani ɓangare na wannan tallafi, an naɗa mata guda 27 a matsayin hadimai na musamman, ɗaya daga kowace ƙaramar hukuma a jihar.

Haka kuma, mata na riƙe da muƙamai masu muhimmanci, ciki har da kwamishinoni mata da kuma mace ɗaya wacce ke riƙe da kujerar mataimakiyar shugaban ƙaramar hukuma a Malam Madori.

Ta jinjinawa Gwamna Namadi bisa goyon bayan da yake bai wa mata a jihar, Hajiya Hadiza ta yi kira ga mata da su ci gaba da marawa wannan gwamnati baya wajen cimma manufofinta domin samun ci gaba mai ɗorewa a Jigawa.

Jihar Jigawa
Comments (0)
Add Comment