Fursunoni 3,590 Na Jiran Hukuncin Kisa A Najeriya – NCoS

Akalla fursunoni 3,590 ne da ke cikin gidajen gyaran hali a fadin Najeriya ke jiran hukuncin kisa, kamar yanda Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta bayyana.

Mai magana da yawun hukumar, Mataimakin ACC Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan a yayin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a yau Laraba a Abuja.

Ya ce adadin jimillar fursunoni a gidajen gyaran hali a fadin kasar ya kai 84,741, wanda ya kunshi maza 82,821 da mata 1,920, kamar yanda yake a ƙididdigar da aka fitar jiya 3 ga Satumba, 2024.

Kakakin ya bayyana cewa jimillar fursunonin da ke jiran shari’a sun kai 57,750, wanda ya kunshi maza 56,303 da mata 1,447.

Da yake bayani kan yanayin kowannensu, ce fursunonin da aka yanke wa hukunci sun kai 21,900, wanda ya kunshi maza 21,519 da mata 381, yayin da wadanda aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai su ne 1,501, wanda ya kunshi maza 1,478 da mata 23.

Jimillar fursunonin da ke jiran hukuncin kisa kuma sun kai 3,517 maza da mata 73, wanda ya kawo adadin zuwa 3,590.

(NAN)

Gidan Gyaran Hali
Comments (0)
Add Comment