Ƴan Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Mata ta Najeriya, Super Falcons, Osinachi Ohale ta karɓi lambar girmamawa a matsayin ƴar wasa mafi ƙwazo a wasan da Najeriya ta buga da Australia ranar Alhamis, wanda Najeriya tai nasara da ci 3 da 2.
Ƴar wasan tsakiyar, Osinachi Ohale ta ce, ita da ƴan uwanta na kulof dinsu na son nunawa duniya irin ƙwazon Najeriya a gasar duniya ta mata wadda FIFA take shiryawa.
Ohale, wadda ta samu lambar yabon kasancewa ƴar wasa mafi ƙwazo a wasan na jiya, ta ce babu wata fargaba a kanta game da cewa ta samu rauni a wasan.
Labari Mai Alaƙa: Dalilina Na Siyar Da Litar Mai Naira 580 A Gidan Maina – Ahmed Musa
“Ina jin cewa ƙalau nake don ban ji wani rauni ba, gaskiya ƙalau nake,” Ohale ta faɗawa wani ɗan jarida mazaunin Birtaniya, Osasu Obayiuwana a filin wasa na Lang Park Stadium.
Da take magana kan canjin dagewar da aka gani a ƴan wasan, Ohale ta ce, ita da sauran ƴan wasan sun yi nufin yin iya bakin ƙoƙarinsu ne a wasan.
“Duk mun yarda da cewa, a gasar cin kofin Afirka na mata ta bara ba mu yi wani ƙoƙari ba, to amma ana dab da fara gasar duniya, duk faɗawa junanmu gaskiya cewar ya kamata mu ƙara ƙoƙari a wasanninmu,” in ji ta.
“Mun yanke cewa, zamu samawa kanmu suna a Australia, kuma ba zai kasance kamar baya ba, zamu nunawa duniya irin ƙwazon da muke da shi da kuma irin ƙarfinmu.”