Gaskiyar Dalilina Na Zaɓar Ƴar’adua Ya Zama Shugaban Ƙasa – Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya ce, ya zaɓi marigayi Shugaban Ƙasa Umaru Musa Ƴar’adua ya gaje shi duk da ya san cewar ba shi da lafiya.

Ya ce, ya ɗau hukuncin ne saboda shawarar masana lafiya da ta nuna cewar, Ƴar’adua wanda aka yi wa dashen ƙoda yana da lafiyar da zai aiki a matsayin shugaban ƙasa.

A wancan lokacin dai, Mataimakin Obasanjo, Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Peter Odili na cikin waɗanda su ka so tsayawa jam’iyyar PDP takarar shugaban ƙasa.

A ƙarshe tsohon janar na soja, Obasanjo ya yanke shawarar yin Ƴar’adua wanda bayan ya ci zaɓe ya rasu a ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 2010.

Da yake magana da jaridar THECABLE, Obasanjo ya musanta zargin da ake yi na cewar da gangan ya dasa ɗantakara marar lafiya don son zuciyarsa.

KARANTA WANNAN: Ƴan Najeriya Na Nadamar Cin Zaɓen Tinubu Da APC, In Ji PDP

Obasanjo ya ce, ya naɗa kwamiti ƙarƙashin marigayi Dr. Olusegun Agagu domin su binciko wanda zai gaje shi, inda su ka yi nazari kan sunaye da dama da ke gabansu su ka bayar da shawara da sunan Umaru a sama da na kowa.

Babban dalilin da ya sa su ka sanya Ƴar’adua a saman sauran shi ne kimarsa da kuma sanin cewar shi ba zai yi sata ba.

Obasanjo ya ƙara da cewar, an bijiro da maganar lafiyarsa a lokacin, inda ya miƙa bayanan lafiyar ga ƙwararre a harkar lafiya ba tare da ya san wane ne ake tambayar a kan sa ba.

Ya ce, bayan ya yi nazarin rahotannin da ya samu, ƙwararren ya gano cewar an yi wa wanda ake tambayar a kansa dashen ƙoda, saboda haka babu damuwa a kansa zai zama mai lafiya kamar sauran mutane.

Obasanjo ya ce, wannan ne abin da ya faru, amma duk wasu maganganu da ake yi na cewar ya san Umaru zai mutu yana kan kujerar shugaban ƙasa na ƙarya ne.

ObasanjoUmaru Musa Yaradua
Comments (0)
Add Comment