Ɗanwasan Super Eagles, Ahmed Musa, ya sanar da rage farashin man fetur a gidan mansa na MYCA -7 na Kano daga naira ɗari shida da shirin zuwa naira ɗari biyar da tamanin a kowacce lita.
Ƙwararren ɗan ƙwallon ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter wanda aka tantance.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Kamfanin NNPCL ya sanar da ƙarin kuɗin man fetur zuwa naira 617 a kan kowacce lita.
An rawaito cewa, rage farashin man a gidan man ɗan ƙwallon ya samo asali ne da yunƙurin ɗan wasan na sassautawa masu amfani da ababen hawa a jihar.
Masu amfani da ababen hawa sun yaba da wannan karamci, inda aka jiyo wani mai suna Usman Muhammad yana cewa, “Wannan abin maraba ne; Yanzu zan iya samun rarar kuɗi maimaikon na siya da tsada.”
Shi dai Ahmed Musa, ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne da ke zama ɗan wasan gaba a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Turkish Süper Lig, Sivasspor da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya.