Akalla Almajirai 17 sun rasa rayukansu a wata gobara da ta tashi a wata makarantar allo a karamar hukumar Kaura-Namoda, Jihar Zamfara.
Shugaban karamar hukumar, Mannir Haidara, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga tashar Channels Television a wata zantawa ta wayar tarho a ranar Laraba.
Wani mazaunin yankin, Abdulrasaq Bello Kaura, ya ce gobarar ta faro ne da dare a ranar Talata, inda ta kuma jikkata dalibai 16.
Bello ya bayyana cewa wutar ta tashi ne sakamakon wani katako da aka tanada a makarantar Mallam Ghali Tsangaya.
“Gobarar ta faru ne a Makarantar Malam Ghali, a wajen da suke karatu. Akwai kusan almajirai 100 a gidan, bayan sun fitar da almajiran, sun yi tunanin babu wanda ya rage a gidan,” in ji shi.
Bayanai sun nuna cewa gobarar ta kwashe kusan sa’o’i uku tana ci, inda ta haddasa mummunar hasarar rayukan daliban da suka makale a ciki.
A ranar Laraba aka binne gawarwakin yaran 17 da gobarar ta hallaka.