Gobara Ta Lakume Dukiya Mai Yawa A Kauyukan Jigawa

Gobara ta lalata dukiya ta miliyoyin kudi a kauyukan Malamawar Dangoli, Karangi da Kwalele da Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa.

Gobarar da ta faru a ranar Lahadi, ta lalata gidaje tare da kona dabbobi, kayan gona da sauran dukiyoyin al’ummar kauyukan.

Wata tawagar ‘yansanda da jami’an kashe gobara daga bangaren jihar da kuma na Filin Jirgan Saman Dutse ne suka isa kauyukan domin kashe gobarar.

Mai magana da yawun ‘yansandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya bayyana cewa, ba a samu rasa ran mutum ba a gobarar, sai dai akwai wadanda suka gudu domin tsira wadanda ba a gansu ba.

Wakilin DAILY TRUST ya rawaito cewa, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Ibrahim Abdullahi El-Y Gumel ya ce, kone karare da ke ajjiye a kauyukan da wasu mutane da ba a san sub a suka yi shine ya jawo tashin gobarar.

El-Y Gumel ya kuma yi kira ga al’ummar da su dena kona dazuka da bololi da ke kusa da garuruwa a wannan zamanin na rani.

GobaraJigawa
Comments (0)
Add Comment