Daga Yaseer Ahmad, Dutse
Tawagar Gwamnatin Tarayya ƙarkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, sun ziyarci Jihar Jigawa domin isar da saƙon ta’aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu dangane da mummunar gobarar tanka da ta hallaka mutane sama da 160 tare da jikkata wasu 96 da yanzu haka suke jinya a asibitoci.
Tawagar ta ƙunshi shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamna Abdulfatah Abdurrahman AbdulRazaq na Jihar Kwara, Ministan Tsaro Muhammed Badaru Abubakar, da Darakta Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar.
A lokacin, sun kai ziyarar gani da ido wurin da gobarar ta faru.
Haka kuma, sun ziyarci waɗanda suka tsira daga hatsarin suna jinya a asibiti sannan suka ziyarci cikin garin Majia don yi wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu ta’aziyya.
Da yake magana da manema labarai, Sanata Akume ya bayyana cewa sun kawo ziyarar ne domin isar da ta’aziyyar Shugaba Tinubu ga iyalan da abin ya shafa, gwamnatin jihar, da kuma al’ummar Jigawa baki ɗaya.
Ya nuna alhininsa kan wannan babban rashi, tare da tabbatar da cewa za a gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin domin ganin an ɗauki matakan kariya daga irin wannan masifa a nan gaba.
“Shugaban kasa ya tausaya sosai ga girman wannan rashi da aka yi, kuma ya bayar da umarni ga Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa da ta hanzarta kawo dauki. Gwamnatin Tarayya za ta haɗa hannu da Gwamnatin Jihar Jigawa don magance wannan al’amari da kyau,” in ji Akume.
Shi ma Gwamna Abdulfatah AbdulRazaq, wanda ya wakilci Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, ya bayyana ta’aziyyar kungiyar ga gwamnatin Jigawa da al’ummar jihar.
Ya jaddada bukatar inganta dokokin tsaro a kan titunan ƙasa, inda ya ce, “Za mu tattauna wannan batu a taron gwamnoni domin nemo hanyoyin aiwatar da matakan tsaro masu inganci a tituna.”
A nasa bangaren, Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gode wa Shugaba Tinubu, gwamnonin jihohi, da dukkan ƙungiyoyi da kamfanoni masu zaman kansu da suka taya jihar alhini kan wannan mummunan lamari.
Ya yaba da yadda aka nuna haɗin kai da goyon baya daga ɓangarori daban-daban bayan faruwar wannan hatsari.
Haka kuma, jam’iyyu da cibiyoyi da dama, ciki har da Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Hedikwatar Tsaro, da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, sun aika da sakon ta’aziyyarsu ga Gwamnatin Jihar Jigawa bisa wannan mummunar gobara ta tanka.