Gwamna Abba Kabir Zai Samu Goyon Bayan Ma’aikatan Jihar Domin Yin Tazarce

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya reshen Jihar Kano (NLC) ta bayyana goyon bayanta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya ci gaba da mulki a karo na biyu, tana mai yabawa da kishinsa ga jin daɗin ma’aikata da ƴan ritaya a jihar.

Shugaban NLC na Kano, Comrade Kabiru Inuwa ne ya bayyana hakan yayin bikin ranar ma’aikata ta shekarar 2025 da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke cikin birnin Kano.

Comrade Inuwa ya jinjinawa Gwamnan bisa kasancewarsa na farko da ya aiwatar da sabon albashi mafi ƙaranci na ₦71,000 a Najeriya, yana mai cewa wannan matakin jarumtaka ne da bai taɓa faruwa ba a tarihin ƙasar, musamman ganin halin tsadar rayuwa da ake ciki.

Ya ce gwamnatin Abba ta tabbatar da biyan albashi da fansho a kan lokaci ba tare da jinkiri ba, tare da biyan bashin fansho na Naira biliyan 16 da ya gada daga gwamnatin baya.

Haka kuma ya yaba da ƙarin mafi ƙarancin fansho daga Naira 5,000 zuwa Naira 20,000 wanda ya bayyana a matsayin wata alama ta kulawa da dattawa da kuma mutanen da suka ba da gudunmawa wajen cigaban jihar.

Ya ƙara da cewa ɗaukar sabbin malamai aiki, amincewa da ƙarin girma da kuma zuba jari a ɓangaren horar da ma’aikata su ma sun taimaka matuƙa wajen farfaɗo da aikin gwamnati a jihar.

“Waɗannan nasarori ba alƙawura bane kawai, a’a su ne shaidu na gaskiyar kishin Gwamna ga ma’aikata; Gwamna Yusuf ya cancanci amana da goyon bayan ma’aikatan jihar,” in ji Comrade Inuwa, yayin da aka bayyana bikin a matsayin sabon zamani na gwamnatin da ke sauraron muradun jama’a.

Comments (0)
Add Comment