Gwamna Namadi Ya Ce APC Za Ta Ci Gaba Da Inganta Rayuwar Jama’ar Najeriya

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa gwamnatin jam’iyyar APC daga matakin ƙasa har zuwa ƙaramar hukuma za ta ci gaba da gudanar da ayyukan raya ƙasa da inganta rayuwar al’umma kamar yadda aka saba tun farkon mulkin jam’iyyar.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin taron “Gwamnati da Jama’a” da aka gudanar a ranar Lahadi a garin Guri, inda gwamnatin jihar ke kai irin wannan taro zuwa dukkan kananan hukumomin jihar 27 domin bayyana ayyukan da ta gudanar da kuma karɓar ƙorafe-ƙorafe da bukatu daga al’umma.

A jawabin da ya gabatar bayan na ɗan majalisar jiha mai wakiltar Guri, Hon. Sulaiman Musa Kadira, da shugaban ƙaramar hukumar, Musa Shu’aibu, Gwamna Namadi ya bayyana cewa, “Jama’ar Guri sun amsa lallai ayyukan da aka faɗa an aiwatar da su,” wanda ke nuni da gamsuwar jama’a da ƙoƙarin gwamnati.

Gwamnan ya karɓi kundi na buƙatun al’umma daga wakilan yankin, yana mai cewa, “Wannan kundi da aka miƙa na bukatun al’ummar Ƙaramar Hukumar Guri, zamu duba wannan kundi, dukkan abin da ya dace zamu aiwatar.”

WANI LABARIN: Matsalar Tsaro Na Neman Lalata Ci Gaban Noman Shinkafa A Auyo, Jihar Jigawa

Taron ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar APC daga matakai daban-daban ciki har da Sanata Ahmad Abdulhamid Malam Madori, dan majalisar wakilai Hon. Abubakar Hassan Fulata da tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Faruk Adamu Aliyu.

Wannan taro ya kasance wata dama ga al’ummar Guri wajen nuna damuwarsu da buƙatunsu kai tsaye ga gwamnati tare da tabbatar da goyon bayan da suka nuna wa gwamnatin APC bisa ayyukan da suka gani da ido.

Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ci gaba da ba da fifiko ga buƙatun jama’a, yana mai cewa, gwamnatin sa ba za ta yi watsi da buƙatun da ke a gabanta ba.

Comments (0)
Add Comment