Gwamna Namadi Ya Dakatar Da Kwamishinan Harkoki Na Musamman Saboda Zargin Aikata Biɗala

Gwamna Malam Umar Namadi ya amince da dakatar da Auwalu Danladi Sankara, Kwamishinan Harkoki na Musamman nan take yayin da ake jiran binciken da ake gudanarwa kan zarge-zargen da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano take masa.

Sanarwar dakatarwar ta fito ne daga bakin Malam Bala Ibrahim, Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, a ranar Asabar.

Sanarnwar ta ce, an yanke wannan hukunci ne sakamakon zarge-zargen da aka gabatar wanda ya sa aka ga ya zama dole a gudanar da cikakken bincike don tabbatar da gaskiya da kare martabar gwamnatin jihar.

Malam Bala Ibrahim ya jaddada ƙudirin gwamnati na kasancewa mai gaskiya da bin ƙa’idojin aiki ƙarƙashin jagorancin Gwamna Namadi.

“Dakatarwar wani mataki ne na kariya don ba da damar gudanar da bincike na adalci,” in ji Ibrahim.

“Muna ɗaukar duk wasu zarge-zarge da muhimmanci kuma mun tsaya kan tabbatar da gaskiya ga al’ummar Jihar Jigawa dangane da wannan gwamnati.”

Zarge-zargen da suka kai ga dakatarwar sun haɗa da rahoton kama Sankara da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano dangane da wani al’amari da ya shafi wata matar aure, tare da yiwuwar fuskantar tuhumar da ta shafi laifukan miyagun kwayoyi.

Dakatarwar Sankara na nufin tabbatar da gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya yayin da ake ci gaba da gudanar da binciken.

Jihar Jigawa
Comments (0)
Add Comment