Gwamna Namadi Ya Naɗa Ƙwararrun Masu Ba Shi Shawara Guda 6

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da naɗin Ƙwararrun Masu Ba Shi Shawara guda shida.

Sanarwar naɗin na ƙunshe ne a sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jiha, Malam Bala Ibrahim ya sanya wa hannu, sannan Jami’in Hulɗa da Jama’a na ofishinsa, Isma’il Ibrahim Dutse ya raba wa manema labarai a yau Juma’a.

Sanarwar ta bayyana naɗin Dr. Risilan Abdul’aziz Kanya a matsayin Ƙwararren Mai Bayar da Shawara kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi ta Hanyar Fasahar Sadarwa ta Zamani; sai Malam Isah Sirajo a matsayin Ƙwararren Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Lafiya da kuma, Dr. Saifullahi Umar a matsayin Ƙwararren Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Noma.

KARANTA WANNAN: Sanata Malam Madori Ya Fi Kowa Temakawa Ɗalibai A Yankin Jigawa Ta Gabas

Sauran sun haɗa da Dr. Muharaz Muhammad Nasir a matsayin Ƙwararren Mai Bayar da Shawara a Fannin Muhalli; sai Engr. Dr. Surajo A Musa a matsayin Mai Bayar da Shawara kan Lantarki da Sabbin Hanyoyin Samun Makamashi; da kuma Dr. Abdullahi Dogo Abubukar a matsayin Ƙwararren Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Ilimi.

Malama Bala Ibrahim ya ce, an yi naɗin ƙwararrun bisa cancanta, ƙwarewa da kuma halaye na-gari.

Ya kuma yi kira ga waɗanda aka naɗa da su yi aiki tuƙuru wajen ganin an cimma manufofi da tsare-tsaren gwamnatin Jigawa mai ci.

Sanarwar ta ƙara da cewar, naɗin ƙwararrun masu bayar da shawarar ya fara aiki nan take.

Jihar JigawaMalam Umar Namadi
Comments (0)
Add Comment