Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya sanya hannu kan dokar kafa Hukumar Hisbah a matsayin hukuma mai cikakken iko, wadda za ta taimaka wajen daidaita zamantakewa da karfafa ɗabi’a mai kyau a fadin jihar.
Wannan mataki ya zo ne kwanaki kaɗan bayan majalisar dokokin jihar ta amince da ƙudirin a zamanta, domin ƙarfafa ayyukan Hisbah a dukkan ƙananan hukumomin jihar.
A yayin sanya hannu kan dokar a wani ƙaramin taron da aka gudanar a zauren Majalisar Zartaswa ta Jihar, Namadi ya bayyana lamarin da cewa “muhimmin ci gaba ne da ya kammala wani aiki na watanni bakwai zuwa takwas da suka gabata”.
Ya ce, “Yau mun sanya hannu kan dokar Hisbah wadda ke kafa hukumar a matsayin hukuma mai zaman kanta a Jihar Jigawa”.
WANI LABARIN: Tattalin Arziƙin Najeriya Ya Ƙaru Da 3.13% A Farkon 2025
Gwamnan ya bayyana fatan cewa wannan sabon tsarin zai kawo daidaito da ɗa’a a cikin al’umma, tare da jan hankali ga jami’an Hisbah da su riƙa gudanar da aikinsu da tsoron Allah, adalci da sadaukarwa.
Ya yaba wa ƴan kwamitin da ya shirya kafa hukumar bisa ƙoƙari da himma da suka nuna wajen cimma nasarar ƙudirin.
“Ƙoƙarinsu ne ya ba mu damar ganin wannan doka ta tabbata,” in ji shi.
Namadi ya ce, “Kafa hukumar Hisbah da doka ta ba ta kariya da izini zai ƙarfafa aikinta wajen tallata ɗa’a da adalci a tsakanin al’umma.”
A ƙarshe ya bayyana hukumar a matsayin ginshiƙin da zai taimaka wajen gina kyakkyawar rayuwa da inganta ɗabi’un al’umma, inda ya jaddada cewa ma’aikatan hukumar su yi aikinsu da gaskiya da adalci domin samun tasiri mai amfani ga al’umma.