Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da shigar da dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar cikin tsarin inshorar lafiya na JICHMA domin inganta samun kulawar lafiya ga ma’aikatan gwamnati.
An ƙaddamar da shirin ne a ranar Juma’a a ofishin Sakatare Gwamnatin Jiha, Bala Ibrahim, wanda ya ce an sauya dokar JICHMA domin tabbatar da shigar da jami’an gwamnati cikin tsarin.
“An riga an ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa kowane mutum a cikin waɗanda aka naɗa zai iya shiga tsarin inshorar lafiya a cikin kwanaki masu zuwa,” in ji Hamza Maigari, babban sakataren hukumar JICHMA.
WANI LABARIN: Wani Sanata Ya Gwangwaje Manoman Mazaɓarsa Da Dubunnan Buhunhunan Takin Zamani A Jigawa
Dr Kabiru Ibrahim daga ma’aikatar lafiya ta jihar, ya bayyana cewa mutane 500 masu rauni daga kowace mazaɓa cikin mazaɓu 287 sun riga sun amfana da tsarin, kuma za a ci gaba da yin rijista da kuma shigar da bayanansu cikin tsarin kwamfuta.
Maigari ya ƙara da cewa wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnatin jihar Jigawa wajen kyautata rayuwar ma’aikatanta da inganta tsarin kula da lafiya ga al’umma baki ɗaya.