Gwamna Namadi Ya Taimaka Wa Ma’aikatan Kwalejin COE Gumel Da Al’amuran Ilimi A Jigawa 

A wani muhimmin mataki na bunƙasa ilimi da jin daɗin ma’aikata, Kwalejin Ilimi ta (COE) Gumel ta yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, kan matakin da ya ɗauka don magance matsalolin da suka daɗe suna addabar kwalejin. 

Gwamnan ya amince da biyan Naira 17,028,000 don biyan basussukan albashin ma’aikata 203 da aka dakatar da biyan su tun 2003. 

Babban Sakataren Kwalejin, Malam Bala Isyaku ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, yana mai cewa an fara biyan kuɗin a ranar Juma’a, 22 ga Oktoba, 2024. 

An tantance mutanen da suka cancanci karɓar wannan kuɗi ta hanyar amfani da tsarin bankin UBA, amma akwai ma’aikata 14 da har yanzu ba su gabatar da kansu don tantancewa ba. 

Shugaban Kwalejin, Dakta Nura Muhammad Ringim, ya gode wa Gwamna Namadi kan jajircewarsa wajen kawo sauye-sauye a harkar ilimi. 

“Wannan tallafin yana nuna jajircewar Gwamnan wajen magance matsalolin da suka daɗe suna addabar harkar ilimi a Jihar Jigawa,” in ji Dakta Ringim.

Comments (0)
Add Comment