Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya amince da baiwa ma’aikatan jihar da ƴan fansho naira 10,000 duk wata a matsayin wani yunƙuri na rage musu raɗaɗin janye tallafin mai.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ne ya rawaito haka, inda ya ce Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan, Dr. Edgar Amos ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Yola a jiya Laraba.
Amos, wanda shine Shugaban Kwamiti na Musamman kan Rage Raɗaɗin Cire Tallafin Mai a kan Ƴan Jihar ya ce, gwamnan ya kuma amince da a fara biyan ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar mafi ƙarancin albashi na ƙasa daga watan Agusta mai kamawa.
Labari Mai Alaƙa: CIRE TALLAFI: Wata Gwamnatin Jiha Zata Bayar Da Tallafin Naira Dubu 10 Ga Ma’aikatanta
Ya kuma ƙara da cewa, gwamnan ya amince da tanadar da tireloli 70 na masara da tireloli 20 na shinkafa domin rabawa ƴan jihar a kan farashi mai sauƙi.
Ya kuma ce, gwamnatin jihar zat siyo takin zamani tirela 50 domin rabawa ma’aikatan gwamnati a jihar kan farashi mai sauƙi.
Ya ce, gwamnatin jihar ta kammala shirin siyo motocin bus domin jigilar ma’aikata a faɗin jihar.
Amos ya bayyana waɗannan aiyuka a matsayin wasu daga cikin shawarwarin da kwamitin da yake shugabanta ya bayar domin rage raɗaɗin janye tallafin man fetur ga ƴan jihar.