Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya amince da naɗin Abba Muhammad Tukur a matsayin sabon Shugaban Gidan Talabijin na Jigawa, JTV.
Gwamnan ya kuma amince da naɗin Yusuf Adamu Babura a matsayin Shugaban Gidajen Radiyo na Gwamnatin Jihar Jigawa.
Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim Mamsa ya sanyawa hannu wadda Ibrahim Isma’il Dutse, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ofishin Sakataren ya rabawa manema labarai.
Yusuf Adamu Babura kwararren ɗan jarida ne, ya ƙware a aikin radiyo, inda yai aiki da Gidan Radiyon Najeriya na Kaduna sannan ya zama Mai Temakwa Gwamnan Jihar Jigawa a Harkokin Radio daga shekarar 2019 zuwa Mayu, 2023.
Shima Abba Muhammad Tukur ƙwararren ma’aikacin talabijin ne da ya samu horo a BBC, sannan ya riƙe muƙamin Shugaban Sashin Kasuwanci na JTV na tsawon shekaru.
Sanarwar ta bayyana cewa an yi naɗe-naɗen ne bisa la’akari da cancanta da dacewa da kuma halayya ta gari.
Malam Bala Ibrahim Mamsa ya gargaɗi waɗanda aka naɗa da su yi aikinsu cikin adalci gwargwadon manufofi da tsare-tsaren gwamnati.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.