Gwamnan Kano Ya Naɗa Ƙarin Masu Ba Shi Sahawara Guda 14 Da Masu Ba Shi Rahoto Guda 44

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a yau Asabar hya sanar da ƙarin wasu masu ba shi shawara da ya naɗa su 14 da kuma manyan masu ba shi rahoto daga ma’aikatu da hukumomi a jihar su 44.

Wannan sanarwar na ƙunshe ne cikin snarwar da Sakataren Yaɗa Labaransa, Malam Bature Dawakin Tofa ya raba a Kano a yau.

Kamafanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya rawaito cewar, a baya dai gwamnan ya naɗa Masu Temaka Masa na Musamman guda 72, waɗanda a yanzu idan aka haɗa da Masu ba shi Rahoto na Musamman 44 da sabbin Masu ba shi Shawara 14, adadin ya kai mutane 130.

KARANTA WANNAN: NA MUSAMMAN: LGs A Jigawa Sun Gaza Shigar Da Kuɗin Fansho Kimanin Naira Biliyan 3.2

Cikin Waɗannan naɗe-naɗe na gwamnan, mata 12 ne kacal daga cikin mutane 130.

Matan sun haɗa da Hassana Abubakar, Babbar Mai Bayar da Rahoto kan Harkokin Majalissar Tarayya; Hajiya Mariya Sani Karaye da Hajiya Sa’adatu Salisu Yusha’u, Masu Bayar da Rahoto kan Ɓangaren Wayar da Kan Mata; Hadiza Aminu, Ɓangaren Kafafen Sadarwa na Zamani; Zainab Ibrahim D, Ɓangaren Ilimin Firamare da kuma Rabi Hotoro, Ɓangaren Harkokin Mata.

Sauran su ne, Shafa’atu Ahmad (Londonbe), Babbar Mai Bayar da Rahoto kan Ci Gaban Karkara; Jameelat Meemi Koki, Mai Bayar da Rahoto kan Aiyuka na Musamman; Fauziyya Isyaku, Mai Bayar da Rahoto kan Harkokin Mata.

Manyan Masu Bayar da Shawara Mata ga Gwamnan sun haɗa da Dr. Fatima Abubakar Amneef, kan Harkokin Aiyuka na Musamman Ɓangaren Mata da kuma Hajiya Aisha Muhammad Idris, Ɓangaren Samun Wadatar Abinci.

Dawakin Tofa ya ce, dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki nan take.

NAN

Abba Kabir YusufJihar Kano
Comments (0)
Add Comment