Masu HND Zasu Mallaki Shaidar Digiri A Shekara 1 A Sabon Shirin Gwamnati

Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Ƙasa, NBTE, ta ƙaddamar da shirin yin karatu ta yanar gizo ga masu shaidar Babbar Diploma ta Ƙasa, HND, domin su mallaki shaidar kammala digiri a shekara ɗaya.

NBTE ta bayyana cewar, karatun na shekara guda da masu HND zasu yi, zasu yi ne ƙarƙashin kulawar jami’o’in ƙasashen waje da aka tantance.

Shugabar Sashin Yaɗa Labarai ta Hukumar, Fatima Abubakar ta ce, ƙoƙarin da aka sha yi a baya na ganin cewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa, NUC, ta amince da tsarin karatun shekaru biyu ga masu HND domin su samu shaidar Master of Technology bai kai ga nasara ba.

KARANTA WANNAN: BUK Ta Samarwa Ɗalibanta Aikin Da Zasu Na Samun Naira 15,000 Duk Wata

Fatima ta ce, ana tilastawa masu shaidar HND da su yi Diploma ta Gaba da Digiri, PGD, kafin a ba su damar yin karatun Masters a jami’o’i, abun da ko da daga baya sun samu shaidar Digirin Digirgir, PhD. sannan suka so komawa jami’o’i da aiki sai an buƙaci su gabatar da shaidar kammala digiri.

Ta ƙara da cewar, waɗannan dalilai ne suka sa NBTE ƙirƙirar wannan sabon tsarin domin magance wariyar da ake nunawa masu shaidar HND a Najeriya.

NBTE ta kuma roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sanya hannu a ƙudirin dokar da zai cire banbancin da ke tsakanin masu shaidar HND da masu shaidar Digiri a Najeriya.

DigiriHNDNBTE
Comments (0)
Add Comment