Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa, wato National Orientation Agency (NOA), ta nuna damuwa kan wani faifan bidiyon barkwanci da mai sayar da motoci da ake kira da Sarkin Mota ya wallafa a yanar gizo, wanda a ciki ya nuna sabuwar mota Mercedes Benz C300 2023 AI tare da tambayar “Shin ma’aikatan gwamnati za su iya mallakar ki?” sai na’urar AI din motar ta amsa da cewa “A’a! wataƙila sai dai a shekara ta 2062.”
A cewar shugaban hukumar NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu, wannan bidiyo na iya kara haifar da matsin lamba ga al’umma musamman a lokacin da mutane ke fama da ƙalubalen rayuwa da kuma yawaitar son samun kudi da wadata cikin gaggawa ba tare da da aiki tuƙuru ba.
“Zama ma’aikacin gwamnati a Najeriya, kamar yadda yake a sauran ƙasashe, aiki ne mai girma da muhimmanci,” in ji shi.
Ya ce ma’aikatan gwamnati su ne ginshikin ci gaban kowace ƙasa saboda suna bayar da gudummawa wajen tabbatar da cewar duk wani kasuwanci ko kamfani yana samun yanayi mai kyau na samun ci gaba.
KARANTA WANNAN MA: TSARO A NAJERIYA: Shekaru Biyun Farko Na Bola Tinubu, Matsalar Tsaro Na Ci Gaba Da Fin Ƙarfin Gwamnati
Issa-Onilu ya bayyana cewa irin wannan bidiyo na iya rage ƙimar ma’aikatan gwamnati da kuma nuna su a matsayin marasa ƙima a idon jama’a.
Hukumar ta bayyana cewa martaninta ya biyo bayan koke-koke daga jama’a da dama da suka kalli bidiyon tare da bayyana damuwarsu a kai.
Ya kuma ja hankalin masu irin waɗannan shirye-shirye da su dinga lura da kalamansu domin kaucewa cin zarafin wani ɓangare na al’umma.
“Da fatan za a dinga amfani da kalmomi masu kwantar da hankali wajen tallata kayayyaki domin mu gina Najeriya da kowa zai samu kima da mutunci,” in ji shi.
A ƙarshe, ya buƙaci haɗin kai da girmama juna tsakanin masu kasuwanci da ma’aikatan gwamnati domin ci gaban ƙasa.