Gwamnati Ta Dakatar Shugaban Hukumar Kula Ilimin Sakandire Saboda Zargin Cinhanci

An dakatar Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Sakandire ta Kasa, NSSEC, Farfesa Benjamin Abakpa saboda zargin badakalar kudade.

Dakatarwa ta bayyana ne a takardar da Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilimi ta Kasa, Andrew David Adejo ya sanyawa hannu.

Takardar ta umarci Farfesa Abakpa da ya mika ragamar kula da hukumar ga mafi girman mukami a hukumar.

Mai magana da yawun NSSEC, Fatima Bappare wadda ta tabbatar da labarin dakatarwar, ta bayyana cewa, kwamitin gudanarwa na hukumar na zargin Farfesa Abakpa da badakalar kudade abin da ya sa aka ce an dakatar da shi domin a samu damar gudanar da bincike.

Ta kara da cewa, an gayyaci Hukumar Magance Laifuffukan Almundahana a Aiki, ICPC, domin ta gudanar da cikakken bincike kan zargin da akewa Farfesan.

Haka kuma, Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimin ya umarci Babban Daraktan Hukumar, Abdulkareem Ibraheem da ya karbi ragamar kula da al’amuran hukumar har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

NSSEC
Comments (0)
Add Comment