Gwamnati Zata Na Cajar N50 A Kan Duk Hada-Hadar Kuɗin Da Ta Kai N10, 000 A OPay

Bankin Yanar Gizo na OPay ya sanar da sabon haraji na N50 akan duk wata hada-hadar da ta kai N10, 000 ko sama da haka, tsarin da aka samar bisa ga dokokin Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Kasa (FIRS).

Daga ranar Litinin, 9 ga Satumba, 2024, za a fara cajin N50 a kan duk wata hada-hadar da ta kai N10, 000 ko sama da hakan.

A sanarwa da kamfanin ya fitar a yau Asabar, OPay ya bayyana wa abokan huldarsa cewa daga ranar 9 ga Satumba, 2024, za a fara cajin N50 akan duk wani wata hada-hadar kuɗi da aka yi zuwa asusun na ɗaiɗaiku ko na kasuwanci.

Kamfanin ya kara da cewa wannan cajin kuɗin na gwamnati ne ba wata hanyar samun kudin shiga ce ga bankin na OPay ba.

Kamfanin OPay ya bayyana cewa, “Wannan cajin zai na tafiya ne kai tsaye ga Gwamnatin Tarayya kuma ba wata riba ce ga bankin ba.”

Sabuwar dokar cajin kudin ta biyo bayan kokarin Gwamnatin Tarayya na tara kudade daga harkokin kasuwancin yanar gizo ta hanyar dokokin FIRS.

OPay
Comments (0)
Add Comment