Gwamnatin Jigawa Ta Dakatar Da Biyan Ƴan J-Teach, Ta Kuma Gano Malaman Bogi 240 Da Masu Takardun Ƙarya 255

Gwamnatin Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta sanar da dakatar da biyan dukkan malaman da suke koyarwa a makarantun jihar ƙarƙashin shirin J-Teach.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa ne ya bayyana hakan ga ƴanjaridu yayin da yake jawabi kan sakamakon tattaunawar Majalissar Zartarwar Jihar.

Dakatar da albashin ƴan J-Teach ɗin ya biyo bayan karɓar rahoton kwamitin da aka ɗorawa alhakin duba yanda za a mayar da malaman na dindindin.

Kwamishinan ya ce, rahoton ya gabatar da bayanan da aka miƙawa tsohon gwamnan jihar, Muhammad Badaru Abubakar a ranar 9 ga watan Mayu, 2023 wanda yai nuni da bankaɗo malaman bogi 240 a cikin ƴan J-Teach da kuma wasu 255 masu takardun bogi, da ma wasu 72 da ba su da takardar komai.

Sagir Musa ya ƙara da cewa, an samu maimaituwar sunayen wasu ƴan J-Teach ɗin da kuma canja nagartattun ƴan J-Teach da waɗanda ba su da nagarta.

Ya kuma ce an gano cewar wasu ƴan J-Teach ɗin kwata-kwata ba sa zaman Jihar Jigawa, yayin da wasu suka ɗau hayar wasu suna riƙe musu aikin.

Ya bayyana cewar waɗannan matsaloli sun jawo ruguje jarabawar da aka yi wa ƴan J-Teach ɗin kafin a ɗauke su aikin.

Ya ce, an dakatar da biyan ƴan J-Teach ɗin albashin ne har sai sabon kwamitin da aka naɗa kan lamarin ya kawo rahotonsa nan da sati huɗu masu zuwa, inda za a biya bashi ga duk waɗanda ba a samu da matsala ba.

J-TeachJihar Jigawa
Comments (0)
Add Comment