Gwamnatin Jihar Kano za ta raba littattafai miliyan uku ga ɗaliban da su ke karatu a makarantun gwamnati da ke jihar.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Umar Haruna Doguwa ne ya bayyana hakan a yau, yayin shirin BBC Hausa na ‘A Faɗa A Cika’, wanda aka gudanar a Kano.
Kwamishinan ya bayyana cewar, abu na kan gaba a tsarin gwamnatinsu na bunƙasa harkar ilimi shi ne gyara ajuzuwa 99 a duk shekara.
Ya ƙara da cewar, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarni da a gina rukunin gidajen malamai a dukkanin makarantun firamare da ke faɗin Jihar Kano.