Gwamnatin Tarayya Ta Rufe Shafukan TikTok, Facebook, Instagram Da X Miliyan 13.6, Ta Share Batutuwa Miliyan 58.9

Gwamnatin Tarayya ta sanar da rufe kusan asusun social media miliyan 13,597,057 tare da share batutuwan ciki guda miliyan 58,909,112 a TikTok, Facebook, Instagram da X saboda “cin zarafi da karya ƙa’idojin aiki” na dandamali.

A cewar Hadiza Umar ta NITDA, rahoton bin doka na 2024 da NCC, NITDA da NBC suka fitar “ya nuna ƙoƙarin dandamalin wajen kare masu amfani da intanet daga cutarwa,” inda aka rubuta ƙorafe-ƙorafe dubu 754,629.

Ta ƙara da cewa “an cire abubuwa 420,439 sannan aka sake ɗora su bayan ɗaukaka ƙara daga masu amfani da shafukan,” abin da ke nuna tsari na tantancewa da daidaita hukunci.

Sanarwar ta jaddada cewa “miƙa waɗannan rahotanni muhimmin mataki ne wajen gina yanar gizo mai aminci da alhakin amfani ga ƴan Najeriya.”

Haka kuma an nuna cewa manyan kamfanoni kamar Google, Microsoft da TikTok “suna bin ƙa’idar rajista a Najeriya da cika wajibin haraji” a ƙarƙashin Dokar Ƙa’idojin Aiki (Code of Practice).

NITDA ta ce, “gina fagen dijital mai lafiya na buƙatar haɗin kai na dindindin tsakanin gwamnati, masana’antu, ƙungiyoyin farar hula da al’umma, tare da haɓaka ilimin dijital.”

Ta ce rahotannin sun ƙara bayyana gaskiya da amincewa kan yadda ake yaƙar abun cikin cutarwa a intanet.

Comments (0)
Add Comment