Gwamnatin Tarayya Ta Ce A Dinga Amfani Da Harsunan Uwa A Koyarwa

A jiya Alhamis ne wani babban jami’in Ma’aikatar Ilimi ya ce, Gwamnatin Tarayya za ta inganta amfani da harsunan uwa wajen koyarwa, musamman a a makarantun firamare da ƙaramar sikandire.

Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi, David Adejo ne ya bayyana hakan a wani shiri da aka gudanar a Abuja, Babban Birnin Tarayya a ranar Alhamis din nan, inda ya ce, wannan yunƘuri na nufin ƙara zaburar da sha’awar yara wajen koyon harsunan asali domin gujewa ɓatan asali da riƙo da al’adu.

Labari Mai Alaƙa: Ƙara Kuɗin Makaranta; Anya Kuwa Ba A Tsokano Wata Fitinar Ba?

A cewar Adejo, yin magana da harshen uwa na ɗaukaka kyawawan ɗabi’u na magabata ba wai kawai nuna asalin mutum ba.

Jami’in ya ce, ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin mutum ko al’umma yawanci yana da alaƙa da amfani da harshensa na asali.

Ya yi kira da a inganta da kuma kare harsunan asali ta hanyar ingantattun manhajoji na makarantu da tsare-tsare masu inganci.

Harshen UwaIlimi
Comments (0)
Add Comment