Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Tsarin Rage Haraji Da Kashi 50% Don Taimaka Wa Kamfanoni Ƙara Albashi

A ƙoƙarin rage matsin lambar rashin isar kuɗi na ma’aikata masu ƙaramin albashi da inganta ci gaban tattalin arziki, Gwamnatin Tarayya ta gabatar da ƙudirin doka da zai ba da damar rage haraji na kashi 50% ga kamfanonin da ke ƙara albashi ko bayar da kuɗaɗen sufuri ga ma’aikatansu.

Wannan ƙudirin doka na daga cikin garambawul ɗin haraji mai faɗi wanda aka tsara yi don amfanin ma’aikata da masu ɗaukar aiki, kamar yanda jaridar PUNCH ta rawaito.

Ƙudirin dokar da aka gabatar a ranar 4 ga Oktoba, 2024 – mai taken “Ƙudirin Dokar Soke Dokokin Haraji da Haɗe Tsarin Dokokin Haraji, da Kafa Dokar Haraji ta Najeriya Don Harajin Kudi, Mu’amaloli, da Kayan Aiki, da Kuma Sauran Abubuwan Da Suka Shafi Haraji” – na da nufin ƙarfafa ƙarin albashi ta hanyar samar da muhimmin rangwamen haraji ga kamfanonin da suka cancanta.

Yanda Tsarin Zai Kasance

Duba ƙudirin a ranar Juma’a ya nuna shirin gabatar da rangwamen haraji na musamman kan masu biyan albashi.

Kamfanonin da suka ƙara albashi ko suke ba da kuɗaɗen sufuri ga ma’aikata masu karɓar N100,000 ko ƙasa da haka a wata, za su sami damar a rage musu haraji da kashi 50%.

An tsara wannan matakin ne don rage matsi ga ma’aikata masu ƙaramin albashi tare da ƙarfafa kamfanoni don su saka jari wajen tallafawa ma’aikata.

Amma dai, wannan tsarin bai shafi ma’aikatan da ke samun sama da N100,000 a wata ba.

Wannan ya dace da dabarar gwamnati na tallafawa ma’aikatan da ke samun ƙaramin albashi kai tsaye.

A wani mataki na girmama aikin yi, ƙudirin ya kuma ƙunshi samar da rangwamen haraji ga kamfanonin da suka ƙara yawan ma’aikatansu a cikin shekarar 2023 da 2024.

A cewar ƙudirin dokar, kamfanonin za su cancanci ragin haraji kan albashin sabbin ma’aikata, idan wannan ƙarin ya haifar da ci gaban yawan ɗaukar aiki.

Domin kamfanoni su cancanci morar wannan tsari, dole ne a tafi da sabbin ma’aikatan na tsawon aƙalla shekaru uku ba tare da an kore su ba.

Haraji
Comments (0)
Add Comment