Ministan Harkokin Jiragen Sama da Bunƙasa Hanyoyin Sararin Samaniya, Festus Keyamo ya umarci dukkan jiragen sama da su bar filin jirgin na Murtala Muhammed International Airport, MMIA, da ke Lagos daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2023.
Ministan ya ce hakan ya zama dole, domin a bayar da dama wajen samun cikakken gyara a filin jirgin.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin ziyarar gani da ido da ya kai filin jirgin a Lagos, inda ya samu rakiyar Shugaban Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya, FAAN, Kabir Yusuf Muhammed.
KARANTA WANNAN: JUYIN MULKIN NIJAR: Ƴan Arewa Na Asarar Naira Biliyan 13 Duk Sati
A jawabinsa lokacin ziyarar, ministan ya umarci dukkan kamfanonin jiragen sama da sauran kamfanonin da ke amfani da filin jirgin da su koma tasha ta 2 (MMIA Terminal 2) na filin jirgin.
Festus Keyamo ya kuma dakatar da duk wani aikin kwangila da sauran aiyukan da ake yi a filin jirgin.