Bincike ya nuna cewar, cikin shekaru uku masu zuwa, bashin da ake bin Najeriya zai kai naira tiriliyan 118.37.
Wannan adadi dai an same shi ne daga lissafin yanayin bashin da ake da shi a yanzu da kuma hasashen kuɗeɗen da za a kashe a matsakaicin zango na shekarun 2024 zuwa 2026.
Wannan ƙididdiga ta nuna cewar Gwamnatin Tarayya ta shirya ciyo bashin naira tiriliyan 26.42 a tsakanin shekarar 2024 da 2026.
Tsarin ta’ammuli da kuɗaɗen na shekara-shekara ya kuma nuni da cewar, biyan bashin da Najeriya zata yi zai laƙume naira tiriliyan 29.92 a cikin shekaru ukun.
Ƙididdigar ta Gwamnatin Tarayya ta yi nuni da cewar, a shekarar 2024, gwamnati ta shirya ciyo bashin naira tiriliyan 7.81, a inda zata ciyo bashin naira tiriliyan 6.04 daga ciki daga cikin gida da kuma naira tiriliyan 1.77 daga masu bayar da bashi na ƙasashen waje.
A shekarar 2025 kuma, Gwamnatin Tarayyar ta shirya ciyo bashin naira tiriliyan 8.54, inda zata ciyo bashin naira tiriliyan 6.42 daga masu bayar da bashi na cikin gida da kuma bashin naira tirilyan 2.12 daga masu bayar da bashi na ƙasashen waje.
Sai kuma a shekarar 2026, inda Gwamnatin Tarayyar ta shirya ciyo bashin naira tiriliyan 10.07, wanda ya haɗa da naira tiriliyan 8.94 daga masu bayar da bashi na cikin gida da kuma naira tiriliyan 1.13 daga masu bayar da bashi na ƙasashen waje.
Lissafi ya nuna cewar, Gwamnatin Tarayyar na ƙoƙarin rage kwaɗayinta na ciyo bashi daga masu bayar da bashi na ƙasashen waje tare da mayar da kwaɗayin bashin nata kan masu bayar da bashi na cikin gida.
Tun a rabin farko dai na wannan shekarar, tsakanin watan Janairu da watan Yuni, Najeriya ta ciyo bashin naira tiriliyan 5.05 daga cikin naira tiriliyan 9.62 da ta shirya ciyo wa a bana.
A ƴan kwanakin nan dai, Ofishin kula da basussukan Najeriya ya ce adadin kuɗaɗen da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 87.38 a ƙarshen watan Yunin da ya gabata.
Wannan adadi dai ya samu ne bayan ƙarin kaso 75.29 wanda ya kai kwatankwacin naira tiriliyan 37.53 a kan abun da ake da shi a ƙarshen watan Maris na bana.
Ƙaruwar yawan bashin ta samo asali ne saboda ƙarin bashin naira tiriliyan 22.7 da Babban Banki ya bai wa Najeriya a bana, da kuma ƙaruwar naira tiriliyan 13.38 da aka samu a kan bashin saboda faduwar darajar naira wadda ta shafi basussukan da aka ciyo daga waje.
Da wannan adadi na bashin naira tiriliyan 87.38 da ke kan Najeriya a yanzu haka, da kuma bashin naira tiriliyan 4.57 da gwamnati zata iya ciyo wa kafin ƙarshen wannan shekarar, da ma naira tiriliyan 26.42 wanda ƙasar ta shirya ciyo wa a shekaru uku masu zuwa, bashin da ake bin Najeriya zai kai naira tiriliyan 118.37 zuwa ƙarshen watan Disambar shekarar 2026 kenan.