Gwamnatin Tarayya ta amince da sauya tsarin wasu tsofaffin kwangilolin hanyoyi tare da ƙarin sabbin ayyuka da darajarsu ta kai Naira tiriliyan 1.81, ciki har da naira biliyan 760.4 da kuma wata kwangila ta dala miliyan 651.7 don hanyar 7th Axial Road da ke haɗa tashar jirgin ruwa ta Lekki zuwa Sagamu-Ore.
Ministan Ayyuka, Dave Umahi, ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa karo na 25 ƙarƙashin shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya ce “an sake fasalin hanyar Akure zuwa Ado Ekiti zuwa kilomita 15 a darajar naira biliyan 19.407, saboda ƙarancin kuɗin da ke akwai.”
Haka kuma, an rage tsawon hanyar Sokoto-Zamfara-Katsina-Kaduna daga kilomita 175 zuwa 82.4 tare da gadoji guda shida a kan kuɗi naira biliyan 105 da aka tsara tun farko.
WANI LABARIN: Ƙananan Hukumomin Kano Za Su Haɗa Naira Miliyan 670 Don Sayen Sabbi da Gyaran Motocin Sarkin Kano
Ministan ya kuma bayyana cewa an sake tsara hanyar Maiduguri zuwa Mongonu a matakai, inda za a fara da kilomita 30 a kan naira biliyan biliyan 21, kafin a ci gaba da sauran kilomita 75 a wani lokaci na gaba.
Dangane da hanyar Aba zuwa Ikot-Ekpene, Umahi ya ce “an amince da matakin farko a kan naira biliyan 30.23,” yayin da gyaran gabar teku ta Ebute-Ero a jihar Lagos, wadda ke barazana ga sansanonin soja da na rundunar ruwa, ya ƙaru daga naira biliyan 114 zuwa naira biliyan 176.495.
Umahi ya ƙara da cewa an bayar da sabbin kwangiloli guda huɗu da suka haɗa da gina gadar sama daga Abakaliki zuwa Afikpo a kan naira biliyan 25, titin Ikoga–Atan–Ado‑Odo a Ogun a kan naira biliyan 37.045, Enugu–Onitsha a kan naira biliyan 150, da kuma naira biliyan 187 don sauran kilomita 96 na Benin–Shagamu–Ore.
A cewarsa, “hanyar ta Lekki Deep Sea Port tana da mahimmanci wajen jigilar kayayyaki daga matatar Dangote da masana’antar takin zamani zuwa jihohin kudu da arewa,” inda ya tabbatar da cewa an samo kuɗin daga China Exim Bank bayan buƙatar hakan daga Shugaba Tinubu a Beijing.
Umahi ya kuma bayyana cewa aƙalla kashi 70 cikin 100 na aikin titin gaɓar teku na Lagos-Calabar ya kammala, yayin da wasu bankunan waje suka yaba da tsarin kwangilar.