Gwamnatin Tarayya Za Tai Ruwan Tallafin Kuɗaɗe Ga Gidaje Miliyan 2.2 Kafin Ƙarshen Agustan Nan

Ƙaramin Ministan Harkokin Jin Ƙai da Rage Talauci, Tanko Sununu, wanda ya tattauna a cikin shirin Sunrise Daily na Channels Television a yau Litinin 18 ga Agusta, 2025, cewa gwamnatin tarayya ta shirya rabon tallafin kuɗi ga iyalai talakawa domin rage talauci a faɗin ƙasar.

“A cikin ƴan kwanaki masu zuwa, kafin ƙarshen watan Agusta, za mu kai ga gidaje 2.2 miliyan,” in ji Sununu, yana mai cewa za a fara aikawa da kuɗin nan da nan.

Ya ƙara da cewa tsarin tantancewa zai kasance ƙarƙashin National Social Safety-Net Coordinating Office (NASSCO), inda, kamar yadda ya faɗa, “Tsarin shi ne NASSCO zai tantance ƴan Najeriya masu rauni bisa ƙananan rukunkun su a cikin rajistar zamantakewar ƙasa.”

Ministan ya jaddada cewa an riga an samu ci gaba a ƙarƙashin shirin Conditional Cash Transfer (CCT), inda ya ce, “Zuwa yanzu, mun riga mun raba Naira biliyan 419 ga ƴan Najeriya miliyan biyar.”

Ya ƙara fayyace yadda akai rabon a ƙasar, yana mai cewa, “Mun rarraba kashi 71 cikin ɗari a Arewa da kashi 21 cikin ɗari a Kudu,” alamar ƙoƙarin da ake yi wajen kai taimako ga yankunan da suka fi buƙata.

Hukumar ta ce an saka sama da gidaje miliyan biyu a cikin rajistar zamantakewa waɗanda za su samu wannan tallafi, lamarin da gwamnati ke fatan zai rage raɗaɗin hauhawar farashin kayayyaki da matsalolin tattalin arziƙi ga matalauta.

Duk da haka, Sununu ya yi kira ga ƴan Najeriya da su yi haƙuri yayin da ake kammala matakai na tantancewa da tabbatar da gaskiyar bayanai, tare da jaddada cewa gwamnatin za ta ci gaba da bibiyar yadda ake rabon don tabbatar da gaskiya da adalci.

Comments (0)
Add Comment