Gwamnatin Tarayya Zata Sauƙaƙa Hanyar Samun Asusun Bankuna Ga Waɗanda Ba Su Da Su

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana tsare-tsaren gwamnantin tarayya domin rage talauci da matsalar tsaro a faɗin ƙasa ta hanyar shigar da ƴan Najeriya cikin harkokin samun kuɗaɗe.

Fadar ta bayyana cewar akwai muhimman tattaunawa da ake yi domin fito da tsare-tsaren yanda za a shigar da ƴan Najeriya marassa amfani da banki cikin tsarin amfani da bankuna.

Fadar ta bayyana cewar, wannan na cikin muhimman abubuwan da ke tsarin manufar gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ne ya bayyana wannan ƙudiri na Fadar Shugaban Ƙasar a wajen buɗe taron horarwa kan amfani da bankuna jiya a Abuja.

Taron horarwa da aka shirya a kwanaki biyu da suka hada da yau Alhamis da gobe Juma’a a Fadar Shugaban Ƙasa, na da nufin wayar da kan masu ruwa da tsaki wajen faɗaɗa harkokin hada-hadar kuɗaɗe a duk faɗin ƙasa.

Sanata Ibrahim Hassan Hadejia
Comments (0)
Add Comment