Gwamnatin Tinubu Ta Mayarwa Da Kwankwaso Martani Kan Zargin Nuna Wariya Ga Arewa

Fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi na cewa, gwamnatin Tinubu na nuna wariya ga yankin Arewa.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa kan sauya tsarin kundin tsarin mulki da aka gudanar a Kano, inda ya ce albarkatun ƙasa sun fi karkata zuwa Kudu, lamarin da ke ƙara jefa Arewa cikin talauci da rashin tsaro.

Ya ce “har yanzu hanyoyin gwamnati a Arewa suna nan a taɓarɓare sosai,” yana mai ba da misalin yadda ya tsinci kansa a kan titin Abuja zuwa Kano a mota bayan jirgin da zai hau ya fasa tasowa, kuma ya kwatanta tafiyar da “tafiya mai wahalar gaske.”

WANI LABARIN: PDP Ta Sanar Da Rana Da Wajen Zaɓen Sabbin Shugabanninta

A martanin da ya wallafa a dandalin X, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce zargin Kwankwaso ba shi da tushe.

“Zargin cewa an yi watsi da Arewa ba gaskiya ba ne, domin gwamnatin Tinubu ta fara aiwatar da manyan ayyuka a yankin da suka shafi tituna, noma, lafiya da makamashi,” in ji Dare.

Ya lissafa manyan ayyuka da suka haɗa da titin Abuja–Kaduna–Kano, Sokoto–Badagry Super Highway, da bututun gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano.

Dare ya ƙara da cewa akwai shirin haɓaka darajar noma da ya kai dala miliyan 158.15 a jihohin Arewa, da kuma aikin Kolmani a Bauchi da Gombe, gami da aikin ACReSAL na farfaɗo da hekta miliyan ɗaya na ƙasar noma da ta lalace.

Comments (0)
Add Comment