Gwamnoni Ba Abun Yarda Ba Ne Kan Tallafin Da Za A Rabawa Talakawa – NLC

Ƙungiya Ƙwadago ta ƙwanƙwashi Gwamnatin Tarayya kan sakin kuɗi naira biliyan 180 ga gwamnonin jihohi a matsayin kuɗin tallafawa talakawa wajen magance matsalolin da janye tallafin man fetur ya tsunduma shi a ciki.

Ƙungiyar Ƙwadago, NLC, da Ƙungiyar Ƴankasuwa, TUC sun tabbatar da cewar, gwamnoni ba abun yarda ba ne, inda suka ce, ƴan siyasa ne zasu yi kashe mu raba da kuɗaɗen ba talakawa ne zasu amfana ba.

A jiya Alhamis ne, Gwamnatin Tarayya ta sanar da sakin naira biliyan 5 ga kowacce jiha da Babban Birnin Tarayya, sannan kuma ta sanar da aika tirololin shinkafa 180 ga jihohin a matsayin wani yankin na rage raɗaɗin ƙwalawar da ƴan Najeriya ke yi saboda janye tallafin man fetur.

Janye tallafin da ya jawo tsananin tsadar man fetur, ya sanya tashin gwauron zabi a kan farashin kayan abinci da biyan kuɗin aiyuka, abun da ya jefa miliyoyin ƴan Najeriya cikin matsanancin talauci da taɓarɓarewar tattalin arziƙi a ƙasa.

KARANTA WANNAN: JANYE TALLAFI: Jihohi Zasu Samu Naira Biliyan 5 Kowaccensu A Matsayin Tallafi

Lamarin ya kuma jawo zanga-zangar gamagari a duk faɗin ƙasa wadda ƙungiyoyin ƙwadago suka shirya, waɗanda suka nemi da a gyara matatun mai na Najeriya a matsayin matakin ɗauka kafin janye tallafin man.

To amma da yake sanar da sakin tallafin rage raɗaɗin a ƙarshen zaman Majalissar Tattalin Arziƙi na Ƙasa na 135 wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya jagoranta, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewar, an bai wa kowacce jiha naira biliyan 5 ne domin gwamnonin jihohin su tanadi buhu dubu 100 na shinkafa, da buhu dubu 40 na masara da takin zamani domin magance matsalar ƙarancin abincin da ake fama da shi a ƙasa.

Zulum ya ƙara da cewar, duba da yanda farashin kayan abinci ke ci gaba da tashin gwauron zabi a ƙasa, Gwamnatin Tarayya a makon jiya, ta saki tirelolin shinkafa biyar-biyar ga kowacce jiha domin rabawa talakawa.

Ku Bi Mu A TELEGRAM Domin Bibiyar Dukkan Labaranmu: t.me/taskaryancihausa

GwamnoniJanye Tallafin MaiTsadar Rayuwa
Comments (0)
Add Comment