A yau Asabar ne Ƙungiyar Gwamnonin Yankin Arewa Maso Gabas suka koka kan watsin da suka ce an yi da yankin.
Gwamnonin sun yi ƙorafin cewa, rashin samun aiyukan Gwamnatin Tarayya a yankin ya yi ƙamari.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne a zaman tattaunawarsu karo na goma wanda suka gabatar a Jihar Bauchi.
A takardar bayan taro wadda shugaban gwamnonin, Farfesa Babagana Zulum ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da bai wa yankin muhimmanci wajen samar masa da cigaba.
Cikin koken da gwamnonin ke da su har da batun rashin wutar lantarki a yankin, inda suka kushe ƙoƙarin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya na yin gyare-gyare a yankin, inda suka ƙara da cewar zasu jira zuwa wa’adin ranar 27 ga watan Mayu da aka saka a matsayin lokacin da wutar lantarki zata dawo yankin.