Gwamnonin Da Ke Son Shiga Haɗakar ADC Na Tsoron Ƙuntatawa Daga Gwamnatin Tinubu

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana cewa tsoron gallazawa da tsangwama daga ɓangaren gwamnati na hana gwamnoni shiga sabon gungun ƴan adawa da aka ƙaddamar domin fuskantar gwamnatin Tinubu a zaben 2027.

Kakakin jam’iyyar na riƙon ƙwarya, Bolaji Abdullahi, ya bayyana haka ne a taron faɗaɗa haɗin gwiwar siyasa na ƙasa (na Arewa) karo na uku da aka gudanar a Abuja ranar Asabar.

Ya bayyana cewa, “Ba lallai ne mu matsa wa wani gwamna ba, domin mun san babu gwamnan da zai so ya shigo yanzu saboda irin tsangwamar da ake musu.”

Ya bayyana cewa wasu gwamnoni suna nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu ne kawai don su kauce wa barazana daga masu mulki, yana mai cewa, “Abin da ke faruwa wata maƙarƙashiya ce a kan talakawan Najeriya.”

WANI LABARI: Ministan Ayyuka Ya Mayar Da Zazzafan Maratani Ga Kwankwaso, Ya Kuma Buƙaci Ya Ba Wa Tinubu Haƙuri

Tun ranar 1 ga Yuli ne fitattun ƴan adawa irinsu Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai suka bayyana goyon bayansu ga ADC a matsayin sabon dandalin adawa, tare da naɗa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaban riƙo da sakataren jam’iyyar.

Duk da wannan, babu wani gwamna mai ci da ya shiga jam’iyyar tun bayan kafuwarta, lamarin da Abdullahi ya danganta da tsoron barazana da ƙuntatawa daga gwamnati.

Ya jaddada cewa jam’iyyar ADC ba za ta zama ƴar amshin shatan wani ɗan siyasa ba, yana mai cewa, “ADC ba za ta bari a mallake ta ba, kuma ba jam’iyya ce da aka kafa don wata manufa ta mutum ɗaya ba.”

Abdullahi ya ce ba su fara tattaunawa kan wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ba tukun, domin burinsu yanzu shi ne gina jam’iyyar da za ta iya ceto Najeriya daga halin da take ciki.

A ƙarshe, ya bayyana cewa an shirya irin wannan taro a kudancin Najeriya don ɗaukar matakan da za su fuskanci ƙalubalen da yankunan ke fuskanta.

Comments (0)
Add Comment